22 Janairu 2020 - 20:26
Za a Gudanar Da Taron Malamai ‘Yan Gwagwarmaya  A Iraki

Za’a gudanar da taron malamai ‘yan gwagwarmaya a Iraki don yada al'adun juriya da sadaukarwa tsakanin malamai, matasa a dukkan bangarorin rayuwa.

  Shugaban kungiyar malaman Sunna na Iraki a ya yin wata ganawa da ya yi da shugaban sashen al’adun na Iran da ke Iraki,ya sanar da gudanar da taron malamai ‘yan gwagwarmaya don karawa juna sani akan juriya da sadaukarwa a tsakanin matsa da malamai a cikin ko wane bangare na rayuwa Iraki.Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti-ANBA-ta rawaito shugaban majalisar malamai ta Iraki shekh Khalid Mula a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa shugaban ofishin kula da al’adu na Iran dake Iraki kan shahadar Kasim Sulemani da Abu Mahdi wadanda shugaban ‘yan ta’adda na duniya ya yi sanadin shahadarsu.Malamin yace; yanzu muna cikin shirin shirya wani taron kara wa juna sani tsakanin malamai ‘yan gwagwarmaya a Iraki ta yada za’a yada al’adar juriya da sadaukarwa a tsakanin matasa da malamai a bangarori daban da daban na rayuwa a Iraki.